• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

HARI KAN JIRGIN RUWA-ISRAILA TA NA BUKATAR MAJALISAR DINKIN DUNIYA TA DAU MATAKI KAN IRAN

Biyo bayan mummunan harin da Iran ta kai kan jirgin ruwan wani dan kasuwar Israila, kasar ta yahudawa na bukatar majalisar dinkin duniya ta kai matakin ladabtarwa kan Iran.

Ministan wajen Israila Yair Lapid ya baiyana muradin kasar sa kan harin da Iran ta kai kan jirgin a arewacin tekun Indiya inda matuka jirgin biyu su ka rasa ran su.

Lapid ya ce ya umurci jami’an diflomasiyyar kasar su yi amfani da duk hanyoyin su wajen ganin majalissar dinkin duniya ta dau mataki kan Iran da ya ce na tafka aiyukan ta’addanci da barazana kan sufurin teku.

Amurka ta zaiyana da cewa an kai shi ne da amfani da jirgin marar matuki.

Masu sharhi na alakanta harin da cewa ramuwar gaiya ce kan harin da Israila ta kai a wani sansani a Shams da Iran ke amfani da shi wajen kare gwamnatin Bashar Al’Asad.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “HARI KAN JIRGIN RUWA-ISRAILA TA NA BUKATAR MAJALISAR DINKIN DUNIYA TA DAU MATAKI KAN IRAN”
 1. Havе you ever thought about writing aan e-book or guest aᥙthoring
  on other sites? I have a blog Ƅаsed on the same ideas you discuss and would love to
  have you share some stories/infοrmation. I know my subѕcribers would νalue your work.

  If you’re even remotely interested, feel free to shoot
  me an e-maіl.

  Loooқ at my webb sjte Georgia

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *