• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

HAR YANZU MALAMAI DA DALIBAI NA JUYAYIN RASUWAR SHEIKH ZARBAN

Har yanzu manyan malaman Islama da daliban ilimi na cikin kaduwa da juyayin rasuwar Sheikh Zarban Alghamidy.

Marigayin wanda limami ne a masallacin Quba a Madina, ya zama babban bango ga daliban ilimi a jami’ar musulunci ta Madina.

Almarhum Zarban wanda aminin limamin masallacin Manzon Allah ne Sheilkh Abdullahi Khuzaifi ya ba da gudunmawa marar misaltuwa wajen samun tarbiya da ilimin ga manyan malaman ahlussunnah a Najeriya.

Manyan malaman irin su shugaban majalisar malamai na Jibwis Dr.Ibrahim Jalo Jalingo, Dr.Sani Umar Rijiyar Lemo, Dr.Mansur Sokoto, Dr. Ibrahim Rjiyar Lemo, Dr.Ibrahim Disina, marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam duk sun amfana daga kogin ilimin marigayin.

Dr.Jamil Sadis ya zaiyana marigayin da cewa fasahar sa tamkar hadari ne da ya hada gajimare ya zubar da ruwa amma ashe ruwan ilimi na fasahar baitukan Sheikh Zarban.

Marigayi ya kan zo Najeriya da kuma jagorantar daukar dalibai don karatu a Madunatul Munawwara.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.