• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

HAR YANZU BA A BAIYANA SAKAMAKON BINCIKE KAN ABBA KYARI BA

Har yanzu rundunar ‘yan sandan Najeriya ba ta baiyana sakamakon bincike kan Abba Kyari ba da hukumar bincike ta Amurka ta zarga da hada kai da babban dan damfara Ramon Abbas wanda a ka fi sani da Hushpuppi.

Tun bayan mika sakamakon binciken da kwamitin rundunar ya yi ga babban sufeto Usman Baba Alkali a ke sa ran jin bayanan da kwamitin ya gano na ko Kyari ya tsallake rijiya da baya ko da sauran magana.

In za a tuna sanarwa daga kakakin rundunar Frank Mba ta baiyana cewa za a nazarci rahoton da tura bayanan ga sassan da su ka dace don daukar mataki na gaba.

Tuni a ke ta raderadi da ba sassauci ga Abba Kyari tun da tuni a ka dakatar da shi daga aiki don gudanar da bincike ba katsalandan.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “HAR YANZU BA A BAIYANA SAKAMAKON BINCIKE KAN ABBA KYARI BA”
  1. When someone writes an paragraph he/she keeps the plan of a user
    in his/her brain that how a user can understand it. Thus that’s why this paragraph is
    amazing. Thanks!

Leave a Reply

Your email address will not be published.