• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

HANA KASUWAR CANJI DALA BA ZAI TAIMAKAWA RAGUWAR TSADA BA-TSOHON AKANTA

Masana tattalin arziki a Najeriya na cewa hana kasuwar canji dala da babban banki ya yi ba zai hana tashin farashin dalar ko wadatar ta a kasa ba.

Tsohon Akanta a hukumar tashar teku Isa Tafida Mafindi ya ce matakin babban bankin na tura kudin ketare bankunan kasuwanci zai kara ta’azzara lamura ne don su ma cibiyoyin neman riba ne ba tare da wani la’akari da cigaba ko koma bayan tattalin arzikin kasa ba.

Mafindi wanda Yariman masarautar Muri ne a jihar Taraba, ya nuna fargabar matukar babban bankin bai sauya tunani ba, to zuwa karshen shekarar nan ta 2021 dalar za ta iya kaiwa Naira 1000 daga sama da Naira 500 yanzu.

Tsohon akantan ya bukaci gwamnan babban bankin Godwin Emefiele ya sauya wata dabara don wannan zai yi wuya ta kai Najeriya tudun mun tsira.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *