• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

HAFSOSHIN TSARO SUN BAIYANA A MAJALISAR DATTAWAN NAJERIYA

Bayan gaiyata daga majalisar dattawan Najeriya, hafsoshin tsaro sun baiyana gaban majalisar inda su ka yi ganawar bayan fage.

Da alamun hafsoshin sun yi bayani ne kan halin tabarbarewar tsaro da matakan shawo kan lamarin da su ke dauka.

‘Yan majalisar sun baiyana shirin ganawa da shugaba Buhari don shaida ma sa abun da su ka gano da hanyar mafita.

Zai yiwu ma majalisar ta amince da wani kasafin kudi matukar hafsoshin tsaron sun bukaci haka.

Akwai fahimtar juna tsakanin shugabancin majalisar da fadar Aso rock amma tabarbarewar tsaron ya sanya wasu ‘yan majalisa a inuwar jam’iyya mai mulki na nuna damuwa ga yanda lamura su ka kara tabarbarewa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *