• Sun. Dec 5th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWIWAR MASU SAURAN SHAN RUWA DAGA BOM DIN BEIRUT TA YI SANYI

ByNoblen

Aug 8, 2021 ,

Gwiwar masu sauran shan ruwa daga fashewar makamai a Beirut ta yi sanyi don rashin samun tallafi shekara daya baya akasin.

In za a tuna a bara wasu makamai da ba a adana su yanda ya dace ba a ma’ajiyar tashar teku ta babban birnin Lebanon, Beirut sun fashe inda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutum 200 yayin da dubban mutane su ka rasa matsuguni.

Karar fashewar ta isa har kasar Cyprus.

Wannan akasi ya sanya ala tilas gwamnatin firaminista Hassan Diab ta yi murabus.

Matsin tattalin arziki da ya biyo bayan akasin ya sanya wadanda su ka rasa matsugunai shiga halin rashin tabbas.

Yanzu haka Lebanon na fadi tashin farfadowa bayan samun tallafin fiye da dala miliyan 300 daga kasashen duniya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *