• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNATIN NAJERIYA TA BUKACI HADA KAI DON YAKI DA ZAZZABIN CIZON SAURO

Akalla a kullum mutane kan shiga dakunan shan magani a yankunan Najeriya su nuna baiyana kukan fama da zazzabi wanda yawanci in an gwada ko yin tambayoyi sai a gano zazzabin cizon sauro ne.

Zazzabin dai ya fi yawaita ne a lokacin damuna don yanda ruwa kan kwanta da kan sanya hayaiyafar sauro.
Akwai kimanin mutum miliyan 100 da ke fama da cutar zazzabin cizon sauro a Najeriya inda mutum dubu 300 kan riga mu gidan gaskiya duk shekara.

Zazzabin na sanadiyyar mutuwar kashi 11% na mata masu juna biyu da hakan kan ma yi saurin shafar jarirai.
Wannan zazzabi ne mai zafi da kan kawo ciwon kai, hajijiya da kuma jin dari da kan sa mai fama son zama a rana.
Amfani da gidan sauro, maganin kashe sauro da tsabtace muhalli na taimakawa wajen rigakafin kamuwa da zazzabin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “GWAMNATIN NAJERIYA TA BUKACI HADA KAI DON YAKI DA ZAZZABIN CIZON SAURO”
 1. I’m truly enjoying the design and layout of
  your blog. It’s a very easy on the eyes which makes it much more enjoyable for me to come
  here and visit more often. Did you hire out a developer to create your theme?
  Great work!

 2. Hi, i think that i saw you visited my web site thus i came
  to “return the favor”.I’m trying to find things to enhance my website!I suppose its ok to use some
  of your ideas!!

Leave a Reply

Your email address will not be published.