• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNONIN NAJERIYA ZA SU YI TARO A ABUJA RANAR LARABA

Gwamnonin Najeriya za su gudanar da gagarumin taro a Abuja don duba muhimman lamuran da su ka shafi kasa.
Sanarwar ta fito ne daga shugaban kungiyar gwamnonin 36 gwamnan Ekiti Kayode Fayemi.
Taron ya sabawa tsarin da a ke gudanarwa na zamanin korona bairos, don wannan gwamnonin za su taru ne da kan su a sakatariyar kungiyar a Abuja ba kamar yanda su kan yi taro ta na’ura ba.
Bayan kammala taron, a bayani daga jami’in labarun kungiyar Abdulrazak Barkindo, gwamnonin za su yi wa manema labaru jawabin bayan taro.
Da alamun taron zai tabo lamuran tsaro da tattalin arziki.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.