• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNONIN KUDU MASO GABAR SUN NANATA KIN AMINCEWA DA KIWO A FILI INDA SU KA KADDAMAR DA ‘YAN BANGA

ByNasiru Adamu El-hikaya

Apr 13, 2021

Gwamnonin kudu maso gabashin Najeriya sun kaddamar da wata runduna mai taken Ebube Agu (DAMUSA MAI BAN MAMAKI) don daukar matakai ciki har da hana kiwo a fili.

Ebube Agu za ta zama kungiyar ‘yan banga kamar yanda Amotekun ta ke a yankin kudu maso yamma.

Gwamonin sun gudanar da taron a garin Owerri karkashin jagorancin gwamnan Ebonyi Dave Umahi.

Gwamnonin sun nuna rundunar za ta rika sintiri don inganta lamuran tsaro a yankin na akasarin kabilar igbo.

Yanzu dai ya nuna sassan Najeriya na daukar natakan tsaro don kare muradun yankunan su.

Kwanan nan wasu ‘yan bindiga a jihar Imo su ka harbe ‘yan kasuwa na arewacin Najeriya guda bakwai.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *