• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNONIN KUDANCIN NAJERIYA 17 SUN DAU MATAKIN SOKE KIWO A FILI

Gwamnonin dukkan kudancin Najeriya da su ka hada da yankin yarbawa, Igbo da kabilun kudu maso kudu sun dau matakin soke kiwo a fili da nuna hakan don inganta tsaro ne a yankin.

Gwamnonin sun gudanar da taron a garin Asaba da ke jihar Delta a kudu maso kudanci.

Sauran matakan da gwamnonin ke son a dauka har da tsarin kason arziki da tasirin yankuna kamar batun kirkiro ‘yan sandan jiha.

A bangaren talakawa ko wadanda a ke mulka na yankin yarbawa na son batun sauya tsarin mulkin kasa ne wajen rage karfin gwamnatin tsakiya inda su kuma wasu daga mutanen yankin Igbo ke fargabar raba kasa don kafa kasar Biafra.

Jihohin kudu maso kudu na cin gajiyar biliyoyi daga kaso na musamman na yankuna masu arzikin man fetur.

Taron karkashin jagorancin shugaban kungiyar gwamnonin Rotimi Akeredolu na jihar Ondo, na bukatar a kira taron kasa ne don kowa ya faiyace abun da ke ran sa.

Masana siyasa na alakanta wannan yunkuri da batun zaben 2023.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.