• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNATIN YAMAN TA CAFKE WANI DAN TAWAYEN HOUTHI

Gwamnatin Yaman ta cafke wani mai mubaya’a ga ‘yan tawayen houthi mai suna Hassan Ali Al-Emad.

Emad ya yi shigar burtu na zama dalibi yayin da ya ke dawowa daga Iran ya yi yunkurin shigowa Yaman ta kan iyakar Oman.

Jami’an gadin kan iyaka su ka gano shi don haka su ka Kama shi su ka kai shi garin Al-Ghaydah su ka tsare shi.

Emad dai da a ka haifa a babban birnin Yaman wato Sanaa a 1977 ya taba ficewa daga kasar ya zauna a Lebanon inda daga nan ya shiga Iran ya zauna na tsawon shekaru 20.

Emad na da suffar ‘yan shia ta hanyar sanya bakin rawani kuma ya na cikin ‘yan shia masu amanna da imamai 12 wato DAN ISNA ASHAR ne.

A baya can ya sha bayanan bukatar mutane su mara baya ga tafarkin marigayi shugaban juyin juya halin shia na Iran Ayotallahi Khomeini.

Lokacin da a rundunar taron dangi ta Larabawa ta kaddamar da yakin marawa zababbiyar gwamnatin Yaman ta Abed Rabbo baya a 2015; Hassan Emad ya bukaci a mara baya ga shugaban ‘yan tawayen houthi da Iran ke daukar nauyi wato Abdul Malik Al-Houthi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
5 thoughts on “GWAMNATIN YAMAN TA CAFKE WANI DAN TAWAYEN HOUTHI”
  1. Thank you a lot for sharing this with all folks you really recognise what you are talking about! Bookmarked. Kindly also visit my site =). We can have a link change arrangement between us!

Leave a Reply

Your email address will not be published.