• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNATIN YAMAN DA ‘YAN HOUTHI SUN ZAUNA A BIRNIN AMMAN DON KARAFAFA YARJENIYAR SULHU

Wakilan gwamnatin Yaman da ‘yan tawayen houthi sun zauna a birnin Amman don karfafa yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin sassan biyu.

Wannan yarjejeniyar dai da majalisar dinkin duniya ta ke jagoranci ta hannun jakadan ta Hans Grunberg na da goyon bayan sabuwar gwamnatin Yaman ta Rashad Al-Alimi.

Zaman na duba bude hanyoyin zirga-zirgar sufuri ne musamman a yankin Taiz wanda ‘yan houthi su ka mallake.
Tuni an samu fara tashin jiragen sama daga babban birnin kasar San’a’a zuwa wasu birane inda a ka samu nasara tafiya birnin Alkahira na Masar.

Da alamun daukar matakai masu inganci don kawo karshen yakin basasar Yaman da ya faro tun 2014.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.