• Tue. Nov 30th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNATIN NIJAR TA WAIWAYI AIKIN MADATSAR RUWA A TILLABERY

Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta waiwayi aikin madatsar ruwa a kauyen Kandaji da ke jihar Tillabery da a ka faro aikin tun shekaru 50 da su ka wuce.

Madatsar ruwan dai daga kogin Kwara, za ta zama cibiyar samar da ruwa da kuma makamashin lantarki.

Shugaban kasar Muhammad Bazoum ya ziyarci inda a ke gudanar da aikin inda ya ce nan da wata biyu za a ga aikin ya kankama.

Bazoum ya ba da tabbacin biyan mutanen da aikin ya shafa kudin diyyar rasa filayen su.

Shugaban na Nijar ya ce aikin na da muhimmaci ga kasar kuma an samu kudin gudanar da shi ta hadin guiwa da wani bankin ketare.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *