• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNATIN NAJERIYA ZA TA JINGINAR DA MANYAN FILAYEN JIRAGEN TA

ByYusuf Yau

Aug 13, 2021 , ,

Gwamnatin Najeriya ta faiyace tsarin da ta dauka na ba da jinginar manyan filayen jiragen ga ‘yan kasuwa.

Wannan dai dama ba sabon tsari ba ne da ma’aikatar zirga-zirgar jirage ta dauka don yanayin tsadar gudanarwa ta filayen jiragen.

Ministan sufurin jirage Hadi Sirika ya kwaranye fargabar ma’aikatan filayen jirage na rasa aiki in an ba da jinginar.

Filayen jirage hudu ne lamarin ya shafa da su ka hada da na Murtala Muhammed a Lagos, Nnamdi Azikwe a Abuja, Aminu Kano a Kano da na birnin Fatakwal.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *