• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNATIN NAJERIYA TA SOKE HUKUMOMIN MA’AIKATAR FETUR UKU TA KAFA SABBI BIYU

ByHassan Goma

Oct 20, 2021 , ,

 

Gwamnatin Najeriya ta soke hukumomi 3 na ma’aikatar fetur da maye gurbin su da sabbi don hakan ya dace da sabuwar dokar man fetur da a ka rantaba hannu a kan a watan agusta.

Hukumomin da a ka soke sun hada da na daidaita farashin fetur, kula da kudin da a ke samu daga fetur da ta kula da ribar da a ke samu wato hukumar DPR, PPPRA da PEF.

Karamin ministan fetur Timpre Sylva ya sanar da wannan matakin da kuma tuni an kaddamar da sabbin hukumomin biyu.

Sabbin hukumomin sun hada da na lamuran hako fetur da kuma na kula da hidimar fetur din da a ka samar.

Gwamnati dai za ta cigaba da aiki da ma’aikatan hukumomin da a ka rushe karkashin sabon shugabanci.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “GWAMNATIN NAJERIYA TA SOKE HUKUMOMIN MA’AIKATAR FETUR UKU TA KAFA SABBI BIYU”

Leave a Reply

Your email address will not be published.