• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNATIN NAJERIYA TA SANAR DA RANAKUN BUKUKUWAN KARSHEN SHEKARA

Gwamnatin Najeriya ta aiyana ranakun hutun bukukuwan da a ka saba yi a karshen shekarar miladiyya.


Ranar jumma’ar nan 25 ga watan Disamba ta zama hutun kirsimeti inda litinin mai zuwa 28 ta zama ranar hutun rana ta biyu ta shagulgulan kirsimeti tun da asalin ranar ta fada a ranar asabar da dama hutu ne na karshen mako.


Sanarwa daga ofishin ministan cikin gida Rauf Aregbesola ta kuma aiyana ranar jumma’a ta sama 1 ga watan Janairu 2021 a matsayin hutun sabuwar shekarar miladiyya.


Aregbesola ya yi fatan mabiya addinin kirista za su dabi’antu da halayen hakuri, zaman lafiya da sanin ya-kamata irin na Yesu Kiristi da a ke bukin tuna ranar haihuwar shi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.