• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNATIN NAJERIYA TA NUNA TAKAICIN YANDA TWITTER YA GOGE SAKON SHUGABA BUHARI

Ministan labaru na Najeriya Lai Muhammed ya nuna takaicin gwamnati da yanda kamfanin  sadarwar yanar gizo na twitter ya goge sakon shugaba Buhari kan matakai da ya ke shirin dauka kan ‘yan awaren Biafra.

A sakon shugaban ya nuna ‘yan awaren ba su fahimci ko san illar da yakin basasa ya haddasawa Najeriya ba don haka gwamnati za ta yi mu su magana da harshen da za su fahimta.

Minista Muhammed ya ce kamfanin bai goge miyagun maganganun masu son wargaza Najeriya ba amma ya zabi goge sakon shugaba Buhari.

Don haka gwamnatin Najeriya na daukar twitter na mara baya ga masu son daidaita Najeriya.

Kamfanin twitter ya ce ya goge sakon don ya sabawa wasu daga ka’idojin sa duk da bai faiyace ka’idar ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.