• Fri. Dec 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari...

GWAMNATIN NAJERIYA TA KARAWA ‘YAN SANDA ALBASHI DA KASHI 20%

ByNoblen

Dec 16, 2021 ,

Gwamnatin Najeriya ta karawa jami’an ‘yan sanda albashi da kashi 20% da zai fara aiki daga watan Janairu na 2022.
Ministan ‘yan sanda Muhammad Maigari Dingyadi ya baiyana haka bayan taron majalisar zartarwa na Larabar kowane mako.
Wannan ya nuna duk jami’an ‘yan sanda za su samu Karin akalla kashi 20% na albashin da su ke karba a yanzu.
Ba mamaki wannan ya rage korafin ‘yan sandan na rashin inganci albashi dama kudin fansho bayan ritaya daga aiki.
Dingyadi ya ce wannan masa daya daga bukatun masu zanga-zangar endsars ne da su ka nema cikin bukatu 5 da su ka gabatarwa gwamnati.
 

KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *