• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNATIN NAJERIYA TA KARA YAWAN CAJI DA TA KE YI WA SHUGABAN IPOB NNAMDI KANU

ByNasiru Adamu El-hikaya

Oct 19, 2021
Gwamnatin Najeriya ta kara yawan caji da ta ke yi wa shugaban ‘yan awaren Biyafara na IPOB Nnamdi Kanu da a yanzu ya ke hannun jami’an tsaron DSS.
Sabbin cajin dai guda 7 a gaban babbar kotun taraiya sun hada da cin amanar kasa da kuma ta’addanci.
Jostis Binta Nyako ta ke sauraron shari’ar kuma an dora sabbin cajin kan sharia’r da a ka faro tun 2016 gabanin arcewa da Kanun ya yi lokacin da a ka ba da belin sa.
Kotun za ta dawo zama don cigaba da sauraron karar ranar alhamis din nan mai zuwa 21 ga watan nan na oktoba.
‘Yan awaren IPOB na daukar wasu miyagun matakai na hana fita a kudu maso gabashin Najeriya a ranakun litinin don matsa lamba ga gwamnati wa imam ta sako Kanu ko ta cigaba da sauraron shari’ar sa.
Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “GWAMNATIN NAJERIYA TA KARA YAWAN CAJI DA TA KE YI WA SHUGABAN IPOB NNAMDI KANU”

Leave a Reply

Your email address will not be published.