• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNATIN NAJERIYA TA DAKATAR DA KAMFANIN JIRGIN EMARATS DAGA SHIGOWA NAJERIYA

Gwamnatin Najeriya ta dau matakin sanya kamfanin jirgin saman Daular Larabawa EMARATS a cikin jerin wadanda ta hana su shigowa Najeriya.
Kafin wannan matakin, EMARATS ya samu amincewar Najeriya na sauka a kasar lokacin da a ka dawo da zirga-zirgar kasa da kasa a ranar 5 ga watan nan.
Wannan matakin na da nasaba da yanda Najeriya ta dau salon duk wata kasa da ta hana ‘yan Najeriya shiga kasar ta ko hana jirgin Najeriya sauka a kasar ta, to Najeriya ma za ta ramawa kura aniyar ta.
Sauran kamfanonin jiragen da lamarin ya shafa sun hada da Air France na kasar Faransa, KLM, Lufthansa na Jamusawa da sauran su da adadin su gaba daya ya kai 10.
Yanzu dai Najeriyar ta na tattaunawa da kasashen turai don duba batun dakatar da saukar jiragen su a Najeriya inda ministan sufurin sama Hadi Sirika ya ce taron ya yi nasara.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.