Gwamnatin Najeriya ta sanar da dakatar da kafar sadarwar yanar gizo ta twitter har illa masha Allahu.
Ministan labaru Lai Muhammed ya sanya hannu a kan sanarwar da dama a ka yi sa ran daukar matakin tun lokacin da kamfanin twitter ya goge sakon shugabs Bubari ga ‘yan awaren Biafra da ke kashe jami’an tsaro, ‘yan arewa da kona dukiyoyin gwamnati.
Tuni wannan mataki ys fara aiki don an nemi shafin twitter an rasa inda masu matukar aiki da kafar ta nuna juyayi.
Gwamnatin ta zargi kamfanin twitter da mara baya ga yunkurin miyagun iri na wargaza zaman Najeriya dunkulalliyar kasa.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀