• Thu. May 19th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNATIN NAJERIYA NA SHIRIN TURA KUDURIN KAFA HUKUMAR KULA DA KAYAN DA A KA KWATO DAGA BARAYIN BIRO

ByNoblen

Sep 17, 2020 , , , ,

Gwamnatin Najeriya ta kammala shirin tura kudurin kafa hukumar da za ta rika kula da kayan da a ka kwato daga barayin biro ko a ka sace ta hanyar cin hanci da rashawa. Majalisar zartarwa ta amince da wannan kuduri don abun da ya baiyana cewa akwai bukatar kafa sabuwar hukuma da za ta rika wannan aiki na kula da kadarorin da EFCC ta kwato. Ministan shari’a Abubakar Malami ya fito da bayanin bayan taron majalisar na makon nan.

Dama cikin zarge-zargen da gwamnatin shugaba Buhari ta yi wa mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci Ibrahim Magu har ya kai ga dakatar da shi, akwai batar da kayan da a ka kawo da su ka hada da gidaje wajen 600. Tuni mai ba wa shugaban Najeriya shawara ta fuskar yaki da cin hanci Farfesa Itse Sergey ya nuna rashin amincewa da kudurin da nuna ministan shari’ar na neman rushe hukumar EFCC ne. Sergey ya bukaci ‘yan majalisa da ‘yan Najeriya su ki amincewa sabon kudurin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.