Gwamnatin Najeriya na karin haske kan kudurin dokar da ta tura don amincewar majalisa kan sanya lamuran albarkatun ruwan kasar baki daya su dawo karkashin gwamnatin taraiya.
Ministan ruwa Sulaiman Adamu ya ce lamarin na son inganta lamura ne bisa dokokin da a ke da su don amfanin al’ummar Najeriya. Tuni wasu masu sukar kudurin ke cewa neman mallakewa jihohi ko kananan hukumomi albaraktun ruwan su ne.
Hakanan jihohin da ke kin jinin tsarin kafa RUGA don kiwon shanu, na nuna wata hanya ce ta neman kwace mu su kasa don ba wa makiyaya dama gudanar da lamuran su a bulus.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀