• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNATIN NAJERIYA NA BUKATAR A SANYA KAFAFEN YANAR GIZO REJISTA DA NBC

Gwamnatin Najeriya ta baiyana kuduri a gaban kwamitin majalisar dokokin Najeriya na bukatar a sanya kafafen labarun yanar gizo su rika rejista da hukumar kula da kafafen rediyo da talabijin NBC.

Ministan labarun Najeriya Najeriya Lai Muhammed ya gabatar da wannan bukata a gaban kwamitin ka’idoji na majalisar wakilai.

Dokar za ta ba wa gwamnati damar jan akala da taka birki ga masu amfani da kafofin yanar gizo wajem yada labaru.

Hakan bai zama wani abun mamaki ba, biyo bayan dakatar da aikin kamfanin sadarwar twitter da gwamnatin ta yi, da nuna sai ya samu lasisi da NBC kafin ba shi damar cigaba da aiki a Najeriya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
59 thoughts on “GWAMNATIN NAJERIYA NA BUKATAR A SANYA KAFAFEN YANAR GIZO REJISTA DA NBC”

Leave a Reply

Your email address will not be published.