• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNATIN KASAR YAMAN TA TSAWATARWA HOUTHI KAN AZABTAR DA YAN JARIDA 4 DA SUKE RIKE DASU TUN 2015.

ByNoblen

Aug 30, 2022

Gwamnatin kasar Yaman ta bukaci yan tawayen Houthi da Iran ke marawa baya su dakatar da azabtar da yan Jarida 4 dake tsare a kurkukunsu da gaggauta mikasu asibiti dan duba lafiyar su.

Gwamnatin tace Houthi ta tsare yan jaridar tare da azabtar dasu ba tare da duba lafiyar su da sama musu ingantattun magunguna ba.

Yan jaridar 4 na daga cikin mutum 9 da Houthi ta kama  a hotel dake babban birnin kasar San’a’a a 2015.

Mutum biyar daga ciki sun samu kubuta daga Houthi lokacin musayar fursunoni tsakanin gwamnati da yan tawayen a 2020.

Yan uwa da iyalan mutanen da Houthi ke tsare dasu na bukatar gwamnatin Yaman tasa baki dan duba lafiyar yan uwan nasu, da rashin hakan na iya sanadiyar rasa rayukansu.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
3 thoughts on “GWAMNATIN KASAR YAMAN TA TSAWATARWA HOUTHI KAN AZABTAR DA YAN JARIDA 4 DA SUKE RIKE DASU TUN 2015.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.