• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNATIN KANO TA TAIMAKA TA BAR HARABAR GIDAN ZAKKA-DR.SAIDU DUKAWA

Malamin kimiyyar siyasa a jami’ar Bayero ta Kano Dr.Saidu Ahmad Dukawa ya yi kira ga gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da ya sa baki wajen barin harabar gidan zakka a anguwar Goron Dutse daga rabawa wasu ‘yan kasuwa.

Kiran ya biyo bayan auna harabar da jami’ai su ka yi don gina shaguna don fadada harkar kasuwanci.

Dr. Dukawa ya ce asalin gidan marayun ya samo asali ne zamanin mulkin mareigayi gwamnan Kano Abubakar Rimi kuma a ka gina a matsayin wakafi.

hakanan zamanin tsohon gwamna Ibrahim Shekarau gwamnati ta karbi aron gidan don hukumar marayu da ya wanzu har mulkin gwamna mai ci amma ba a sabunta aron ba har wani sabani ya shigo lamarin a ka tashi ma’aikatan gwamnati daga gidan.

Dr. Dukawa ya shawarci gwamnatin Ganduje da ta karawa gidan zakkar karfi ta hanyar mallaka ma sa shagunan filin.

Hukumar tsara birane ta Kano ta ce ta raba filin ne don korafin da jama’ar anguwar ta turawa majalisar dokoki ta jihar kan yanda a ke miyagun aiyuka da dare a filin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “GWAMNATIN KANO TA TAIMAKA TA BAR HARABAR GIDAN ZAKKA-DR.SAIDU DUKAWA”
  1. I am truly happy to glance at this website posts which consists of tons of valuable facts, thanks for providing these information.

  2. Nice post. I learn something new and challenging on websites I stumbleupon everyday.
    It will always be helpful to read through content from other authors and practice
    something from their sites.

Leave a Reply

Your email address will not be published.