• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNATIN KADUNA TA YI WATSI DA TATTAUNAWA DA WADANDA SU KA SACE DALIBAI

ByNoblen

Apr 6, 2021

Gwamnatin jihar Kaduna ta nesanta kan ta da wasu masu tattaunawa da wadanda su ka sace daliban makarantar gandun daji ta Afaka da nuna ba da izini su ke yin hakan ba.

Wannan na faruwa daidai lokacin da ‘yan ywan dalibai ke bukatar a karbo dalibai ta duk wani mataki mai yiwuwa.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya yi gargadin duk wanda a ka kama da shiga tsakani da masu satar mutanen za a gurfanar da shu gaban kotu.

Gwamnatin Kaduna na da matsayar sam ba ribar ba da kudin fansa ko magana don sulhu da masu satar mutanen.

‘Yan ywan daliban na nuna damuwa cewa tamkar gwamnati ba ta damu da wadanda a ka sacen ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *