• Fri. Jul 1st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

Gwamnatin Buhari ta shiga damuwa kan yadda ake mutuwa daga cutar Maleriya

ByAuwal Ahmad Shaago

Nov 29, 2021

Gwamnatin Najeriya ta bayyana damuwarta kan yadda cutar zazzabin cizon sauro ke hallaka jama’ar kasar Ministan lafiya ne ya bayyana haka, inda yace ana yawan samun mace-mace duk da cewa akwai maganin zazzabin Ya kuma bayyana abubuwan da ka iya jawo kara yaduwar cutar, inda ya kirayi ‘yan Najeriya su kula sosai.

 

 

 

Gwamnatin tarayya ta bayyana damuwarta cewa duk da samun maganin zazzabin cizon sauro na Maleriya, cutar ce ke haddasa mace-macen ‘yan Najeriya da dama.

 

 

 

Don haka ta bukaci dukkan ‘yan Najeriya da su fara gwajin cutar zazzabin cizon sauro kafin fara shan magani.

 

 

 

A watan Oktoban da ta gabata ne hukumar lafiya ta duniya ta shawarci amfani da riga-kafin zazzabin ciwon sauro, inda tace har yara za a iya yi musu.

 

 

 

Ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire ne ya yi wannan kiran a wajen kaddamar da gangamin kawo karshen zazzabin cizon sauro na kasa, mai taken “Mama Put”.

 

 

 

Shirin kawar da zazzabin cizon sauro na kasa (NMEP) tare da goyon bayan shirin shugaban kasar Amurka na yaki da cutar zazzabin cizon sauro (PMI) ya kaddamar da gangamin taimakon gaggawa na zazzabi, da kuma gwada duk masu fama da zazzabi kafin a yi musu magani.

 

 

 

 

Ministan wanda ya samu wakilcin daraktan kula da lafiyar jama’a, Dr Morenike Alex-Okoh ya ce har yanzu zazzabin cizon sauro ne ke kan gaba wajen mace-mace a kasar.

 

 

 

 

Hakazalika, a cewarsa zazzabin cizon sauro ne babbar matsalar lafiyar al’umma, duk da cewa ana iya yin riga-kafinta a yanzu kuma ana iya magance ta.

 

 

 

Ehanire ya ce an samu nasarar ne sakamakon amfani da gidajen sauron da aka fesawa magani, da gaggawar daukar mataki, gwajin zazzabi don tabbatar da cewa ana dauke da zazzabin da kuma amfani da magungunan da suka dace.

 

 

 

Ya kara da cewa kawo karshen zazzabin cizon sauro a kasar zai dakatar da miliyoyin cututtuka da kuma mutuwar dubban daruruwan mutane a duk shekara.

 

 

A cewarsa:

 

 

“Karshen cutar zazzabin cizon sauro zai kara yawan zuwa makaranta, da inganta yawan ma’aikata da rage tsadar lafiyar iyali.

 

 

Za a iya cimma kawo karshen zazzabin cizon sauro.” Mataimakiyar darakta na gangamin Malaria and Tuberculosis, Breakthrough ACTION ta Najeriya, Dokta Bolatito Aiyenigba ta ce manufar NMEP ita ce a samu Najeriya da ba ta da aukuwar zazzabin cizon sauro.

 

 

A kalamanta:

 

 

“Duk da haka, matsalolin halayya da suka hada da jinkirin neman magani ga zazzabin, rashin amincewa da sakamakon gwajin zazzabin da kuma rashin yin jinyarta na ci gaba da kawo cikas ga cimma wannan hangen nesa.”

 

 

 

A cewarta, shirin na “Mama Put” shiri ne da ya kuduri aniyar inganta yadda ya dace a kula da zazzabi a tsakanin ‘yan Najeriya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
4 thoughts on “Gwamnatin Buhari ta shiga damuwa kan yadda ake mutuwa daga cutar Maleriya”

Leave a Reply

Your email address will not be published.