• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNATIN BUHARI TA SAKI AIYUKAN TA NA TSAWON SHEKARU 6 KAN MULKI

Gwamnatin APC ta shugaba Buhari ta saki kundin bayanin aiyukan da ta cimma a tsawon shekaru 6 ta na karagar mulki a fadar Aso Rock.

Gwamnatin da ta hau a 2015, ta dau wasu shekaru ta na aza alhakin lalacewar lamura a kasar kan tsohuwar gwamnatin PDP da ta yi shekaru 16 kan mulki.

Salon caccakar tsohuwar gwamnati ya fara sauyawa zuwa bayanan kalubalen tattalin arzikin duniya, illar ta’addanci da annobar korona.

Hakanan gwamnatin na nuna ta yi nasara wajen daukar matakan yaki da cin hanci har ya kai kasashen ketare na dawo da wasu kudi da barayin biro su ka fitar da su su ka adana a bankunan manyan kasashen.

Gwamnatin na bugin kirji cewa ta bullo da hanyoyin tallafawa jama’a masu yawa ta hanyar lamuni da tallafi fiye da duk gwamnatocin da su ka shude.

Abun da zai zama kalubale mafi girma ga gwamnatin shi ne yanda wasu a yankin kudanci ke tada fitinar neman raba kan kasa ko bullo da tada zaune tsaye ba tare da la’akari da jam’iyya ko wata mu’amala ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.