A karshen watan nan na mayu, gwamnatin Najeriya ta Buhari da akasarin jihohi sun shiga shekara ta uku kan wa’adi.
Wannan na nuna yayin da gwamnatin ta Buhari ke cika shekata ta uku a wa’adin ta na karshe, hakanan gwamnoni da dama kama daga arewa zuwa kudu ke shiga shekara ta uku a wa’adi na karshe.
Akwai kimanin gwamnoni 7 da jihohin su ba sa zabe s lokacin babbsn zabe don yanda hukuncin kotu ya sauya lokutan zaben su.
Masana siyasa da tsoffin ‘yan siyasa na nuna shekarar ta uku ta siyasa don tamkar saura shekara daya a wa’adin a siyasance maimakon shekaru biyu a lissafe.
Hukumar zaben Najeriya INEC tuni ta fitar da jadawalin babban zabe a shekara ta 2023 a kasar da ts samu wanzuwar gwamnatin siyasa tsawon shekaru 22.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀