Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da sauke tuta rabin gora na tsawon kwana uku don karrama babban hafsan sojan kasa Ibrahim Attahiru da tawagar sa da su ka riga mu gidan gaskiya.
Sauke gorar ya fara ne daga litinin din nan zai kammala zuwa laraba.
Hakanan sojoji sun share wunin litinin su na hutun da shugaban ya ba su don juyayin rashin da rundunar ta yi.
Matakin ya biyo bayan caccaka da mutane su ka yi na rashin ganin shugaban ko wani babban jami’i na taraiya a wajen jana’izar marigayan.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀