• Sun. Nov 28th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNATIN BORNO TA DAKATAR DA WATA KUNGIYA DON KOYAR DA HARBA BINDIGA A HOTEL

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya ba da umurnin dakatar da aikin wata kungiya mai zaman kan ta ta kasar Faransa a jihar don samun jami’an ta da laifin koyar da harba bindiga a wani hotel.

Jami’in labarun gwamnan Isa Gusau ya ce an yi bincike inda a ka cafke masu koyar da harba bimdigar a wani sasahe na hotel din a Maiduguri.

Cikin abubuwan da a ka samu akwai bindigogin wasa da kayan dura harsashin da mutanen ke amfani da shi wajen koyar da yanda a ke sarrafa bindiga.

Gwamnan ya umurci a gudanar da bincike kan aiyukan kungiyar mai suna ACTED don gano dukkan bayanan da a ke bukata.

Makwabtan hotel din su ka ba da labarin jin karar harbe-harbe don haka a ka sanar da ‘yan sanda don bincika lamarin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *