• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNATIN AMURKA TA TARA KUNDAYE DA DAMA DON ZAMA HUJJAR ZARGIN ABBA KYARI DA HULDA DA DAN DAMFARA

ByNasiru Adamu El-hikaya

Sep 27, 2021

Hukumar binciken laifuka ta Amurka FBI ta tara kundayen na’ura mai kwakwalwa dubu 2,700 da kuma kundaye takarda dubu 6,700 don tabbatar da zargin aikata laifin hulda da dan damfara da shaharerren dan sanda Abba Kyari ya yi.
Yayin da wadanda a ke kara a lamarin da dan damfara Abbas Hushpuppi su 6 ke bukatar Karin lokaci daga kotu don shiryawa, ita ma gwamnatin Amurka ta bukaci damar don ba ta damar bita kan takardun don nazartar shaidar da a ka daga ketare.
Kundayen sun kunshi bayanai na zantawa ta kafar sada zumunta, muryoyi da sauran sakonni ta yanar gizo na wadanda a ke tuhuma.
Tuni dai mutum 3 da a ka kama a Amurka  na shirye don gurfana gaban kotu, amma sauran mutum uku da su ka hada da DSP Abba Kyari ba sa nan.
Mutum ukun sun samu nasarar dage sauraron karar har watan mayun badi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *