• Tue. Nov 30th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNATIN AFGHANISTAN TA HARAMTA ZANGA-ZANGA

Gwamnatin Afghanistan karakshin Taliban ta haramta duk wata zanga-zanga da nuna don lamuran tsaro ne ya jawo daukar matakin.

Sabon ministan harkokin cikin gida Sirajuddin Haqqani ya baiyana cewa an gano barazana ga rayukan masu zanga-zangar daga wasu da za su iya kulla mu su makarkashiya don haka gara su dakatar da hakan.

Haqqani ya ce duk wata zanga-zanga da ba ta samu amincewar ma’aikatar shari’a ba, haramtacciya ce.

Tun amsar madafun iko a kasar da Taliban ta yi a ranar 15 ga watan jiya, masu zanga-zanga da su ka hada da mata kan fito don nuna kin jinin yanayin jagorancin ‘yan Taliban da ba damar walwala da ta saba da addini ko kuma yanda Taliban ke yanke hukunci bulala ga wadanda a ka samu da laifi.

An ba da labarin wasu ‘yan jarida biyu da su ka hada da Taqi Daryabi da Nemad Naqdi sun sha dukan tsiya a hannun ‘yan Taliban yayin da su ka je daukar labarun zanga-zanga a yankin Karte Char.

‘Yan zanga-zanga na zargin kashe sadarwa INTANET a sassan Kabul don a hana su taruwa ne amma kamfanin sadarwar ROSHAN ya ce matsalolin na’ura a ka samu.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *