• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNATI ZA TA SAKE KUDIN ASUU A CIKIN MAKO DAYA-MINISTAR KUDI ZAINAB SHAMSUNA

ByYusuf Yau

Nov 19, 2021

Ministar kudin Najeriya Zainab Shamsuna ta ce ma’aikatar ilimi ta ba da umurnin a saki kudin da gwamnati ta yi wa kungiyar malaman jami’a ASUU alkawari cikin sati daya.
Wannan ya fito ne a taro da kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamiala ya jagoranta da shugabannin kungiyar don dakatar da yajin aikin da malaman su ka ba da wa’adi.
Yanzu ya nuna gwamnati za ta saki Naira biliyan 30 na gyaran jami’o’in cikin Naira biliyan 220 da za a bayar kashi-kashi.
Kazalika akwai Naira biliyan 22.17 na alawus din malaman.
Yanzu dai da alamun an samu dakatawar barazanar yajin aikin kuma za a jira a ga cika alkawarin gwamnati.
Gabanin dawowa yajin aiki na wannan karo, ASUU ta yi mafi tsawon yajin aiki na wata tara a tarihi da hakan ya kassara karatun dalibai.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.