• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNAN ZAMFARA YA ZIYARCI YANKUNAN DA ‘YAN BINDIGA SU KA KAI HARI

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawallen Maradun ya kai ziyara karamar hukumar Anka da Bukkuyum don duba halin da jama’a ke ciki biyo bayan harin ‘yan bindiga.
Mummunan farmakin daga ‘yan bindigar da a ka ba da labarin na kaura daga Sokoto zuwa jihar Zamfara ya yi sanadiyyar asarar rayuka da daman gaske.
An samu labarin gwamnan ya gana da jagororin sassan tsaro don samun karin bayani kan wannan hari don daukar matakai.
Yanzu haka akwai ‘yan gudun hijira a manyan garuruwan kananan hukuomin biyu da ke samun kayan tallafi.
Hare-haren ‘yan bindiga ya zama ruwan dare a wasu jihohin arewa maso yamma da Neja a arewa ta tsakiya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *