• Tue. Nov 30th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNAN ZAMFARA YA SAUKE JAMI’AN GWAMNATIN SA KAF

Gwamnan jihar Zamfara a Najeriya Bello Matawallen Maradun ya yi garambawul a gwamnatin sa inda ya sauke kowa.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da a ke raderadin gwamnan zai sauya sheka daga PDP zuwa APC a ranar 12 ga watan nan.

Mu’amalar gwamnan da APC da azawa gwamnonin PDP laifin rashin mara ma sa baya, ya kara tabbatar da sha’awar sa ta kaura zuwa APC mai mulki a taraiya.

Maradun ya ce sam sallamar jami’an gwamnatin sa ba shi da nasaba da kaura zuwa APC amma ya yi haka ne don kawo sabon jini da za su nausa jihar tudun mun tsira.

Gwamnan ya ce an samu shekara biyu bisa karaga, ya dawo ya kawo sauyin rabin wa’adi da wasu sabbin jami’an don cika alkawuran kamfen.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *