• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNAN LEGOS YA BI SAHUN MASU HANA KIWO A FILI

ByYusuf Yau

Sep 21, 2021 , , , ,

Gwamnan jihar Lagos Babatunde Sanwo-Olu ya rantaba hannu kan dokar hana kiwo a fili a fadin jihar da hakan ya sanya shi shiga sahun da dama daga gwamnonin kudancin Najeriya da su ka dau irin matakin.
Olu ya sanya hannu kan dokar bayan amincewar bai daya da ta samu daga majalisar dokokin jihar.
Wannan tamkar cika muradin dukkan gwamnonin kudu ne da su ka ajiye zuwa watan nan na Satumba kowace jiha ta kafa dokar hana kiwo a fili.
In ka debe jihar Binuwai, duk jihohin arewacin Najeriya ba su dau irin wannan matakin ba, don akwai jihohin da su ka bude dazuka don kiwon da su ka hada da Gombe, Kano, Kogi da sauran su.
Hakika matakin na gwamnonin kudu ya yi hannun riga da umurnin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi na dawowa da burtalin shanu na tarihi da ke cikin doka a fadin Najeriya.
Za a jira martanin gwamnatin taraiya kan yanda kasar ke samun tsari da ke cin karo da juna kamar ba kasa daya ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *