• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNAN JIHAR ABIA YA DAKATAR DA SHUGABAN MA’AIKATA NA GIDAN GWAMNATI DON KARI DA TULIN NAIRA

Gwamnan jihar Abia Okezie Ikpeazu ya dakatar da shugaban ma’aikata na gidan gwamnatin jihar don yanda a ka ga ya na wasa da kudi ta hanyar yi wa wani fasto yayyafin kudi.

A faifan bidiyon da ya yadu sosai a yanar gizo an ga shugaban ma’aikatan ACB Agbazyere na yayyafawa faston mazaunin Anacha kudi da hakan ya kawo caccaka mai tsanani daga mutane da ke ganin hakan almubazzaranci ne.

Tuni Gwamna Ikpeazu ya nada sakataren gidan gwamnatin jihar Alozie Odoemelam ya karbi aiyukan Agbazuere har sai yanda hali ya yi nan gaba.

Ba sabon abu ba ne yanda jami’an gwamnati ke wasa da kudi a wajajen bukukuwa don burge masu kallo alhali talakawa su na cikin kuncin rayuwa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
16 thoughts on “GWAMNAN JIHAR ABIA YA DAKATAR DA SHUGABAN MA’AIKATA NA GIDAN GWAMNATI DON KARI DA TULIN NAIRA”
  1. Howdy just wanted to give you a quick heads up and let you know a
    few of the pictures aren’t loading correctly. I’m not sure why but I think its a linking issue.

    I’ve tried it in two different web browsers and both show the same outcome.

Leave a Reply

Your email address will not be published.