Gwamnan Borno Babagana Umara Zulum ya ba da tallafin naira miliyan 20 ga iyalin Burgediya Janar Dzarma Zirkushu a Kaduna.
In za a tuna hafsan na soja ya gamu da ajalin sa ne tare da mukarraban a yankin karamar hukumar Askira Uba a jihar Borno yayin kai karin karfi ga rundunar da ke fafatawa da ‘yan ta’adda.
Gwamnan ya jajantawa iyalin marigayin da yaba irin gwagwarmayar da maigidan su ya yi ta hanyar sanya hannu na ta’aziyya a littafin da a ka girke a kasa da babban hoton marigayin.
Jami’in sadarwa na gwamnan Isa Gusau ya ce gwamnan zai tallafawa sauran dakarun ma da su ka riga mu gidan gaskiya tare da Zirkushu.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀