• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNA GODWIN OBASEKI YA LASHE ZABEN GWAMNAN EDO A KARO NA BIYU

Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki ya lashe zaben gwamnan jihar Edo a karo na biyu don mulkin jihar na karin shekaru hudu na karshe. Kamar yanda ya yi nasara a zaben da ya gudana a baya lokacin ya na APC kan dan takarar PDP Ize Iyamu, wannan karo ma ya sake nasara kan Iyamu da ya dawo APC shi kuma a PDP. Zaben na ranar asabar 19 ga watan na satumba, ya nuna Obaseki ya samu kuri’u dubu 307,955 inda Ize Iyamu ya samu dubu 223,619.

PDP ta lashe zabe a kananan hukumomi 14 inda APC ta lashe a kananan hukumomi 4. Jama’a magoya bayan Obaseki sun cika tituna a babban birnin jihar Benin su na nuna murna kan nasara musamman a kan tsohon shugaban APC kuma tsohon gwamnan jihar Adams Oshiomhole. Tuni shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya Obaseki murnar lashe zaben, ya na mai cewa kullum akidar sa ita ce a gudanar da zaben adalci.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “GWAMNA GODWIN OBASEKI YA LASHE ZABEN GWAMNAN EDO A KARO NA BIYU”
  1. always i used to read smaller posts that also clear their motive, and that is also happening with this post which I am reading here.

Leave a Reply

Your email address will not be published.