• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMNA GANDUJE YA KAI ZIYARAR TA’AZIYYA GA TSOHON GWAMNA KWANKWASO

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kai ziyarar ta’aziyya ga tsohon gwamnan jihar Rabi’u Musa Kwankwaso bisa rasuwar kanin sa.
Duk da ziyarar ta ta’aziyya ce amma ganin manyan jami’an siyasar Kano biyu a kan kujera daya su na magana ta kusan kunne, ya sa mutane sun yi ta sharhi kan lamarin.
Rabiu Kwankwaso wanda ba ya shiri da gwamnan tun zaman sa gwamna, ya tarbi Ganduje da mutuntawa da ke nuna ko ba komai sun zauna a inuwa daya albarkacin ta’aziyya.
Gwamna Ganduje ya gana da Kwankwaso bayan kai ziyara mahaifar sa a karamar hukumar Madobi inda ya yi ta’aziyya ga hakimin Madobi Saleh Musa Kwankwaso.
A gidan sa da ke Bompai a Kano, Rabi’u Kwankwaso ya gaiyaci tsohon gwamnan kabarin mahaifin sa da ke cikin gidan inda a ka sake gabatar da addu’a.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *