• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GWAMANTIN NAJERIYA TA SAKE TSAWAITA WA’ADIN HADA LAYIN WAYA DA KATIN DAN KASA

Nimc Logo

A karo na uku gwamnatin Najeriya ta kara tsawaita wa’adin hada layukan salular jama’a da lambar katin shaidar dan kasa mai lambobi 11.

Yanzu dai sabon wa’adin shi ne shida ga watan gobe.

Gwamnatin dai ta bakin ministan sadarwa Isa Pantami ta kara wa’adin don ba da dama ga mutane ‘yan kasa da mazauna kasar su samu damar hada layukan na su bayan samun shaidar.

A kalla dai a sanaddiyyar kara wa’adin an samu sama da layuka  miliyan 56 sun tura bukatar hada layukan na su da shaidar mai taken “NIN”

Gwamnatin ta dau matakin hade layukan da shaidar don magance tabarbarewar tsaro da a kan yi amfani da layukan salula wajen aikatawa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.