• Wed. Jun 29th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GOMMAN MUTANE SUN SAMU RAUNUKA A WATA FASHEWA A SANSANIN PALASDINAWA A LEBANON

ByNoblen

Dec 11, 2021 ,

Wata fashewar makamai a sansanin Palasdinawa a garin bakin teku na Tyre da ke Lebanon ta yi sanadiyyar samun raunuka ga gomman mutane.
An ba da labarin fashewar daga ma’adanar makamai ta Hamas ne da ke sansanin Burj Al-Shemali.
Kungiyoyin Palasdinawa na bangaren Hamas da Fatah na da sansanoni a yankin da hukumomin Lebanon ba sa shishshigi a ciki.
Wani alkali ya ba da umurnin a binciki sanadiyyar aukuwar akasin.
Wata majiya ta ce gobarar ta auku ne sanadiyyar ma’adanan iskar sheka ta taimakawa masu fama da cutar annobar korona.
Kungiyar Hamas dai a hukumance ba ta yi magana a kan wannan lamarin ba.
 

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
60 thoughts on “GOMMAN MUTANE SUN SAMU RAUNUKA A WATA FASHEWA A SANSANIN PALASDINAWA A LEBANON”

Leave a Reply

Your email address will not be published.