• Fri. Dec 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari...

GOBARAR TA TASHI A KAMFANIN FETUR DIN ARAMCO A JEDDAH DAGA HARIN HOUTHI

An samu tashin gobara a babban kamfanin fetur na duniya mallakar Saudiyya wato ARAMCO a Jedda sanadiyyar wani hari da ‘yan tawayen houthi a Yaman da Iran ke marawa baya su ka kai.
Gobarar ta tashi a wani tankin fetur a cibiyar raba man da ke Jeddah kuma ba a samu labarin asarar rai ba.
Harin na zuwa ne daidai lokacin da houthi ta kai hare-haren makami mai linzami a sassa daban-daban na Saudiyya ranar asabar da lahadi.
Harin ya shafi cibiyar hakar fetur ta Yanbu, garin Jazan, Khamis Mushayt da Dhahran.
Hukumomi sun baiyana tare hare-haren da su ka shafi kudancin Saudiyya da ke iyaka da kasar Yaman.
Saudiyya dai na jagorantar rundunar larabawa da ke daukar matakan soja wajen dawo da zababbiyar gwamnatin Yaman ta Abed Rabbo da ke zaune a birnin Aden na kudanci.

KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
33 thoughts on “GOBARAR TA TASHI A KAMFANIN FETUR DIN ARAMCO A JEDDAH DAGA HARIN HOUTHI”
  1. What i don’t understood is actually how you are now not really much more well-appreciated than you might be now. You are so intelligent. You know thus significantly with regards to this subject, produced me individually consider it from a lot of various angles. Its like women and men are not fascinated except it¦s something to do with Lady gaga! Your individual stuffs outstanding. All the time care for it up!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *