• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GOBARA-MANOMA ALBASA A NIJAR NA BUKATAR TALLAFIN GAGGAWA

A yanzu haka manoma albasa a jamhuriyar Nijar na bukatar agajin gaggawa bayab gobara ta lashe hajar su.

Gobarar dai da a ke binciken sanadiyyar ta, ta kone rumbunan albasa 100 da hakan ya sa manoman tagumi.

Tuni manoman da wasu masu fada a ji ke bukatar gwamnatin Muhammad Bazoum ta duba lamarin don tallafawa manoman su koma bakin sana’ar su.

Lamarin gobara dai kan shafi manoma da ‘yan kasuwa musamman a Najeriya inda gobara yawanci daga wutar lantarki kan kone kasuwanni da jefa jama’a cikin damuwar rashin samun tallafin da zai dawo da su bakin sana’a.

Yayin da wasu gobara kan juye ta zama alheri a gare su, wasu daga faruwar ta sun samu karayar arziki sai abun da Allah ya yi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
39 thoughts on “GOBARA-MANOMA ALBASA A NIJAR NA BUKATAR TALLAFIN GAGGAWA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.