• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GIDAN YARI-NA GA SHADDAR DA MUTANE KAN KWANA SU NA BAYAN GARI HAR GARI YA WAYE KAFIN A ZO DA RUWA A KWARA MA TA – IG WALA BAYAN FITOWA DAGA YARI

Mai wallafa labarun yanar gizo IG.Wala ya ce ya ga shadda a gidan yari da fursunoni kan kwana su na bayan gari a ciki kafin da safe a zo da ruwa a bokiti a watsa ma ta ta yi kasa da najasar.

Wala wanda ke magana a taron kungiyar ma’abota kafafen labaru  na wata-wata; a kwanakin baya ya samu ahuwa daga gwamnatin jihar Kebbi bayan shafe shekara daya cikin shekaru 12 da a ka yanke ma sa hukuncin dauri sanadiyyar samun sa da lafin kazafi ga tsohon shugaban hukumar alhazai Barista Abdullahi Mukhtar da kotu a Abuja ta yi.

IG.Wala ya kara da cewa naman miya da a ke ba su a gidan yari duk bai fi girman gyada ba kuma har ma akwai masu cin duk wani tsiron ganye don maganin yunwa.

Kazalika ya ce ba ya fatan ko makiyin sa, ya shiga gidan yari, don akwai wani wari na fitar hankali da kan taso lokacin da a ke kwashe bayan garin fursunonin.

Duk da haka Wala ya ce in mutum ya na da galihu zai samu wajen zama maid an ma’ana da abinci mai dan armashi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.