• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GIDAJEN REDIYO DA TALABIJIN SU GOGE SHAFIN SU NA TWITTER – GWAMNATIN NAJERIYA

Gwamnatin Najeriya ta ba da umurnin gidajen rediyo da talabijin su goge shafukan su na twitter ba tare da wani bata lokaci ba.

Wannan mataki ya biyo bayan dakatar da aikin kamfanin twitter a Najeriya baysn ya goge sakon niyyar dirar mikiya kan ‘yan awaren Biafra/IPOB.

Hukumar da ke kula da gidajen rediyo da talabijin ta Najeriya NBC ta umurci kafafen labarun su daina ambata sunan twitter a cikin labarun su musamman a shirye-shiryen da a ke gabatarwa kai tsaye.

In za a tuna ministan shari’a Abubakar Malami ya ce gwamnati za ta dau matakin shari’a kan duk wanda a ka samu ya na sabawa dokar hana amfani da twitter.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.