• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GBAJABIAMIALA YA ZIYARCI IYALIN MAI SAYAR DA JARIDAR DA DAN SANDAN SA YA BINDIGE

Kakakin majalsar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamiala ya ziyarci iyalin mai sayar da jarida Ifeanyi Okereke a Suleja jihar Neja; wanda dan sanda a tawagar sa ya bindige har lahira.

Lamarin ya auku ne ranar alhamis lokacin da Gbajabiamiala ya fito daga majalisar inda ya tsaya wajen masu sayar da jarida kamar yanda ya saba don gaisawa da su amma daga bisani sai dan sanda a tawagar ya bude wuta da ya sa albarushi da doki kan Okereke ya yi sanadiyyar mutuwar sa.

Kakakin ya kare akasin da cewa run da dadewa dama ya kan tsaya don gaisawa da masu sayar da jaridar da ya ce mutanen sa ne, amma yayin da zo barin wajen sai wasu su ka nemi birkita tafiyar kwambar motocin da ya sanya jami’an sa bude wuta a cikin iska da ya sa harashi ya yi batan kai ya hallaka Okereke.

Gbajabiamiala wanda a ke cewa mai matukar girman kai ne don ba ya amsa gamsuwar mutane ta haka kawai, ya musanta lamarin da cewa ya na girmama mutane ba tare da la’akari da matsayin su ko arzikin su ba.

Kakakin ya ce ya bude wani asusu don kula da ‘ya’yan marigayin ciki har da jinjiri da ba a yi sunan sa ba, har sai sun kai shekaru 21.

Gbajabiamiala ya gaiyaci masu sayar da jarida su zo zauren majalisar a talatar nan don za a karrama marigayin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.