• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

GASKIYA NE NI INA CIKIN FULANI- SHUGABA BUHARI GA OTOM

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba zai kaucewa gaskiyar magana ba cewa ya na daga cikin Fulani kamar yanda gwamnan Binuwai Samuel Otom ke nanatawa in ya zo caccakar gwamnati.

Otom dai ya ce don shugaba Buhari ya na tare da Fulani shi ya sa ya bar su, su ke aikata abun da su ka ga dama.

Shugaba Buhari a zantawa da gidan talabijin na ARISE ya ce hakki ya rataya a wuyan gwamnoni su tashi wajen tabbatar da tsaro  lafiya da dukiyar al’ummar su ba yanda wasu kan rugo fadar Aso Rock da sunan a taimaka mu su.

Shugaban ya ce tun da gwamnonin sun tsaya takara da yi  kamfen din alkawarin ceton al’ummar su, sai su cika alkawarin maimakon bugewa da garzayowa Abuja ko dora laifi kan gwamnatin taraiya.

Hakanan shugaban ya yi bayanin umurnin da ya bayar na dawo da burtalin shanu na asali don makiyaya su samu hanyar wucewa ba tare da shiga gonaki ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “GASKIYA NE NI INA CIKIN FULANI- SHUGABA BUHARI GA OTOM”

Leave a Reply

Your email address will not be published.